Acts 14

A Ikoniyum

1A Ikoniyum Bulus da Barnabas suka shiga majamiʼar Yahudawa yadda suka saba. A can suka yi magana gabagaɗi har Yahudawa da Alʼummai masu yawa suka gaskata. 2Amma Yahudawan da suka ƙi ba da gaskata, suka zuga Alʼummai suka sa ɓata tsakaninsu da ʼyanʼuwa. 3Bulus da Barnabas kuwa suka daɗe sosai a can, suna magana gabagaɗi saboda Ubangiji, wanda kuwa ya tabbatar da saƙon alherinsa ta wurin sa su su aikata ayyuka da alamu masu banmamaki. 4Mutanen birnin suka rarrabu, waɗansu suka goyi bayan Yahudawa, waɗansu kuma suka goyi bayan manzannin. 5Yahudawa da Alʼummai tare da shugabanninsu suka ƙulla shawara a tsakaninsu, domin su wulaƙanta su su kuma jajjefe su da duwatsu. 6Amma suka sami labari suka kuma gudu zuwa biranen Ikoniyum na Listira da Derbe da kuma ƙauyukan kewaye, 7inda suka ci gaba da waʼazin labari mai daɗi.

A Listira da Derbe

8A Listira kuwa akwai wani gurgu zaune a ƙafafunsa, wanda gurgu ne tun haihuwa, kuma bai taɓa tafiya ba. 9Ya kasa kunne yayinda Bulus yake magana. Bulus kuma ya kafa masa ido, ya lura cewa yana da bangaskiyar da za ta warkar da shi 10sai ya ɗaga murya, ya ce, “Tashi ka tsaya kan ƙafafunka!” Da jin haka, sai mutumin ya yi wuf ya kuma fara tafiya.

11Saʼad da taron suka ga abin da Bulus ya yi, sai suka ihu da harshen Likayoniyawa, suna cewa, “Alloli sun sauka mana da siffar mutane!” 12Sai suka ba wa Barnabas, sunan Zeyus, Bulus kuma suka kira Hermes domin shi ne shugaban magana. 13Firist na Zeyus, wanda haikalinsa ke bayan birni, ya kawo bijimai da furanni a ƙofofin birni domin shi da taron mutanen sun so su miƙa musu hadayu.

14Amma da manzannin nan Barnabas da Bulus suka ji haka, sai suka yayyage tufafinsu suka ruga cikin taron, suna ihu suna cewa: 15“Ya ku mutane, don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kawai, ʼyan adam ne kamarku. Mun kawo muku labari mai daɗi ne, muna gaya muku ku juya daga waɗannan abubuwa banza, ku juyo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama da ƙasa da teku da kuma dukan abin da yake cikinsu. 16A zamanin dā, ya bar dukan ƙasashe su yi yadda suka ga dama. 17Duk da haka bai bar kansa babu shaida ba: Ya nuna alheri ta wurin ba ku ruwan sama da kuma amfanin gona a lokatansu; ya ba ku abinci mai yawa ya kuma cika zukatanku da farin ciki.” 18Ko da waɗannan kalmomi ma, da ƙyar suka hana jamaʼan nan yin musu hadaya.

19Sai waɗansu Yahudawa suka zo daga Antiyok da Ikoniyum suka sha kan taron. Suka jajjefi Bulus da duwatsu suka kuma ja shi bayan birni, suna tsammani ya mutu. 20Amma bayan da almajiran suka taru kewaye da shi, sai ya tashi ya koma cikin birni. Washegari shi da Barnabas suka tashi zuwa Derbe.

Komawa Zuwa Antiyok a Suriya

21Suka yi waʼazin Labari mai daɗi a wannan birni, suka kuma sami almajirai da yawa. Sai suka koma Listira, Ikoniyum da kuma Antiyok, 22suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.” 23Bulus da Barnabas suka naɗa musu dattawa a kowace ikkilisiya, tare da adduʼa da azumi, suka miƙa su ga Ubangiji, wanda suka dogara da shi. 24Bayan sun bi ta Fisidiya, sai suka zo cikin Famfiliya, 25kuma saʼad da suka yi waʼazi a Ferga, sai suka gangara zuwa Attaliya.

26Daga Attaliya kuma suka shiga jirgin ruwa suka koma Antiyok, inda dā aka danƙa su ga alherin Allah saboda aikin da suka kammala yanzu. 27Da isarsu a can, sai suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da rahoton duk abin da Allah ya aikata ta wurinsu da kuma yadda ya buɗe ƙofar bangaskiya domin Alʼummai. 28Suka kuma jima a can tare da almajirai.

Copyright information for HauSRK